SARAUNIYAR INGILA TA CE ITA JININ ANNABI MUHAMMAD (SAW) CE - IBN HUJJAH BLOGSarauniyar Ingila ta ce ita jinin Annabi Muhammad (S.A.W) ce
February 2, 2018 4:29 pm
Sarauniyar Ingila Elizabeth ta fara ikirarin cewa, ta fito ne daga tsatsaon Annabi Muhammad Sallallahu Alaihi Wa Sallam inda ta kuma umarci da a yada wa duniya wannan abu.
Wannan yunkuri mai ban mamaki na Sarauniya Elizabeth na tayar da hankali kan tunanin da ake na cewa, watakila kungiyar asiri ta “Illuminati” na matakin karshe na amfani da Addinin Musulunci wajen mulkar duniya ta hanyar amfani da gidan”Windsor”.
Sarauniyar ta zayyana nasabarta inda ta ce, tana mataki na 43 a jerin layin jikokin Annabi Muhammad (S.A.W).
Ana yin ikirarin cewa, iyalan Masarautar Ingila sun fito daga tsatson Sarkin Larabawa na “Seville” da ke Spaniya. Shugabancinsa ya mamaye yankuna da dama da suka hada da Eurosia, Tsibiran Iberia da suka hada da kasashen Spaniya, Portugal, Andorra da Gibraltar.
Daular Seville ita ce ta 5 mafi girma a tarihin duniya wadda ta shugabanci mutane miliyan 62 wato kaso 29 na mutanen duniya a wancan lokacin.
No comments:
Post a Comment