SAHABI DAN SAHABI JIKAN SAHABI BABAN SAHABI ! ! | BANGAREN SAHABBAI | BANGAREN SAHABBAI - IBN HUJJAH FORUM*SAHABI, DAN SAHABI, JIKAN SAHABI, BABAN SAHABI ! ! !*
*Tambaya*
Assalamu alaikum, don Allah akwai sahabin da kakansa sahabi ne, babansa sahabi, dansa kuma sahabi ?, ina son karin bayani malam ?
*Amsa*
Wa alaikum salam.
To malam sahabin da yake kakansa sahabi, dansa sahabi, babansa sahabi, shi ne : Abdurrahman dan Abi-bakr bn Abi Khuhafah kamar yadda Ibnu Salah da Ibnul-jauzy suka ambata. Saboda mahaifinsa Abubakar sahabi ne, hakanan kakansa Abu khuhafah shi ma sahabi ne sannan dansa Muhammad sahabi ne, Ibnu Hajar yana cewa : Ba mu san mutum hudu da 'ya'yansu wadanda suka ga Annabi s.a.w ba sai wadannan.
Abin da yake nufi shi ne : Muhammad da mahaifinsa Abdurrahman da kakansa Abubakar da kakansa na biyu Abu-kuhafah dukkansu sun ga Annabi s.a.w. don haka su kadai suka samu wannan darajar, Allah ya kara musu yarda .
Don neman karin bayani duba tarjamar Muhammad Bn Abdurrahman Bn Abi-bakr Bn Abi-khuhafah a Usudul-gabah a lamba ta : 6083.
*Dr. Jamilu Yusuf Zarewa*
No comments:
Post a Comment