ALHAMDULILLAH YAU ALHAMIS AN FARA SANYA KARATUN MALAM LAWAN A AMINCI RADIO 103.9 - IBN HUJJAH BLOGMuna sanar da ‘yan uwa daga yau Alhamis 01/02/2018 an fara sanya karatun littafin riyadussalihin wanda Mal. Lawan Abubakar Shu’aib (limamin masallacin Triumph) yake gabatarwa a masallachin Abdurrahman bn Auf dake Kofar Wambai a nan Kano a duk ranar laraba,
an fara sanya wannan karatu a sabuwar tashar Radion nan taAminci Radio Don Cigaban Al’umma 103.9 FMda misalin karfe 09:00 zuwa 10:00 na safe,
daman ana sanya wannan shiri da misalin karfe 06:00 zuwa bakwai na safe a tasharRahama Radio Farin cikin a’umma 97.3
No comments:
Post a Comment