MATA MUSULMAI A NIGERIYA SUN BUKACI A KAWO KARSHEN NUNA MUSU WARIYA SABODA SANYA HIJABI - IBN HUJJAH BLOGMata Musulmai a Najeriya sun bukaci a kawo karshen nuna musu wariya saboda sanya Hijabi
February 1, 2018 8:15 am
Mata Musulmai a Najeriya sun gudanar da zanga-zanga inda suka bukaci da a samar da dokar da ta za ta kawo karshen nuna musu wariya saboda Hijabi da suke saka wa.
An gudananar da zanga-zangar karkashin kungiyar “Almu’uminat Foundation” inda suka bukaci Majalisar Dokokin Najeriya da ta samar da dokar da za ta ayyyana nuna wariya, zalunta, cusgunawa da hantarar mata saboda sanya Hijabi a matsayin babban laifi.
Shugabar Kungiyar Ni’imatullahi Quadri ta bayyana wa manema labarai a Legas cewa, Hijabi ‘yancin mata ne da Addinin Musulunci Ya ba su, a saboda haka lokaci ya yi da za a kawo dokar da za ta huknta duk wanda ya nuna musu wariya ko bambanci.
Ta ce, suna son shaida wa gwamnati da ‘yan Najeriya cewa, Hijabi ‘yancinsu ne kuma taken taronsu na ranar 1 ga watan Fabrairu wada rana ce ta Hijabi ta Duniya shi ne”Hijabina ‘Yancina”.
Wannan taro dai ya a daidai lokacin da ake yawan samun cusgunawa mata a a Najeriya saboda suna sanya Hijabi.
A shekarar 2013 ne mai fafutuka Nazma Khan ta kirkiri ranar Hijabi ta Duniya a 1 ga watan Fabrairuinda tun daga sannan ake taruka a ranar a kowacce shekara a kasashen duniya sama da 140.
No comments:
Post a Comment