WELCOME TO IBNHUJJAH NURUL ISLAM

NEWS | SPORTS | CELEBRITY GIST | MIXTAPE | COMEDY VIDEOS | JOKES | TECH | FASHION

PROMOTE MUSIC | ADVERTISE | SUBMIT FREEBEAT

Social Media Widget

IBNHUJJAH NURUL ISLAM

Assalamu Alaikum Barkanku Dai Jama'a, Kuna Tareda Ni Sulaiman Ibn Hujjah. Zaku Iya Shiga Shafukanmu Ta Wadannan Adress Din. http://sulaimanibnhujjah55.xtgem.com http://islamicforum.com.ng

Powered by Blogger.

Categories

Featured post

NEMAN TSARI DAGA ABUBUWA GUDA HUDU. NEMAN TSARI DAGA ABUBUWA GUDA HUDU.

NEMAN TSARI DAGA ABUBUWA GUDA HUDU. 1-Azabar Qabari 2-Azabar wutar Jahannama 3-Fitinar Rayuwa da Mutuwa 4-Fitinar Masihil Dujal... Anna...

Total Pageviews

Search This Blog

Blog Archive

Categories

Categories

Categories

Translate

Ads

Popular Post Of The Weeks...

  • Miyetti Allah Ta Yi Allah Wadai Da Kisan Da Aka Yiwa Wasu Fulani Matafiya a Benue - IBN HUJJAH BLOG
  • Miyetti Allah Ta Yi Allah Wadai Da Kisan Da Aka Yiwa Wasu Fulani Matafiya a Benue - IBN HUJJAH BLOGMiyetti Allah Ta Yi Allah Wadai Da Kisan Da Aka Yiwa Wasu Fulani Matafiya a Benue

    Hadakar kungiyoyin Fulani makiyaya a Najeriya sun bukaci gwamnatin Najeriya da ta hanzarta bincike game da kisan gillar da aka yiwa wasu Fulani matafiya a tashar motar garin Gboko dake jihar Benue.
    Su dai wadanda aka kashen wadanda ke cikin motar haya, sun taso ne daga jihar Adamawa, kuma suna kan hanyarsu ne na zuwa jihar Kogi to amma sai wasu yan bangan tibi, suka far musu da nan take aka kashe mutum bakwai, biyu yanzu haka suna asibiti yayin da biyu kuma ba’a gansu ba.
    Da suke bayyana takaicinsu game da kissan gillar da aka yiwa Fulanin matafiya, hadakar kungiyar makiyayan Najeriya ta Miyetti Allah, ta bukaci gwamnatin Najeriya da ta gaggauta cafke wadanda ke ta hannu a wannan ta’asa.
    Su dai fulanin da aka kashen sun taso ne daga jihar Adamawa su goma sha daya, inda suka dauki shatar mota don zuwa jihar Kogi, to amma kuma sai direbansu ya ratsa zuwa tashar mota ta Gbokon, kuma shigar su ke da wuya sai wasu matasa yan banga suka far musu da nan take suka kashe bakwai daga ciki, biyu kuma yanzu haka ke kwance a gadon asibiti, wanda kawo yanzu ba a ga biyu daga cikin matafiyan ba.
    Da yake tabbatar da faruwan lamarin, Mafindi Umaru Danburam dake zama shugaban kungiyar Miyetti Allah na jihohin arewa maso gabas, ya ce yanzu haka suna cikin halin zulumi na faruwar wannan kisan gillan, inda ma ya bukaci gwamnatin tarayya da ta bincika wadanda ke da hannu a lamarin.
    Shima da yake karin haske, shugaban kungiyar Miyetti Allah a Najeriya, Alhaji Muhammadu Kiruwa Ardon Zuru, ya ce suna da tababa game da abubuwan dake faruwa yanzu a jihar Benue.
    Kakakin rundunar yan sandan jihar Benue Joel Yamu Moses, ya tabbatar da faruwar lamarin, wanda ya aikowa Muryar Amurka da wata sanarwar da rundunar yan sandan jihar ta fitar.
    Sanarwar rundunar yan sandan na cewa, “da missalin karfe tara da rabi rundunan yan san jihar ta sami rahoton cewa, an samu wani hargitsi a tashar motar Gboko, kuma nan da nan aka tura yan sandan to sai dai kafin zuwansu har an kashe Fulani matafiya bakwai, kuma an kona gawarwakinsu. Binciken farko ya nuna wadanda aka kashen matafiya ne dake kan hanyarsu ta zuwa jihar Kogi.Yanzu haka akwai wadanda aka kama kuma ana cigaba da bincike, kuma tuni har an kafa dokar hana fita a garin don tabbatar da doka da oda.”

    No comments:

    Post a Comment